Bincike ya nuna cewa mutane kan yi karatu saboda ɗalilai da dama. A nan ƙasa sai mu duba waɗannan muhimman batutuwa:
Don samun Labari:
Mukan yi karatu don mu samu labari musamman a kan abubuwan da ke faruwa kusa da mu da kuma waɗanda ke da nisa da mu na yau da kullum. Mukan samu irin waɗannan labarai ta hanyar karanta jaridu. Ke nan ta hanyar karanta jaridu mukan wayar da kan mu.
Don Nishaɗi:
Yawancin mutane sukan yi amfani da lokacin hutawarsu wajen karanta ƙagaggun labarai don nishaɗi.
Don Neman Takardar Shaida:
Makaranci kan yi karatu don ya cimma burinsa na neman takardar shaida wadda zai riƙa amfani da ita a rayuwarsa. A nan, ana bukatar makaranci da ya karanta zaɓaɓɓun littattafai musamman waɗanda suke cikin manhajar ajinsa da nufin in ya gama karanta su za a gwada shi, in ya cancanta za a ba shi takardar shaida.
Don Tara Sababbin Kalmomi Da Kuma Keɓaɓɓun Kalmomi:
Makaranci kan yi karatu don ya tara da kuma gane ma’anar ke~a~~un kalmomi da kuma sababbin kalmomi da ya haɗu da su a yayin karatu. Wannan kan taimaka wa makaranci ainun wajen gane keɓaɓɓun kalmomi na fanni dabam-dabam.
Tambayoyi Me ake nufi da kalmar karatu?
Ku Lissafa aƙalla dalilan yin karatu guda uku.
Ku bayyana biyu daga cikin dalilan yin karatu da kuka ambata a tambaya ta biyu.