Muhimmancin Rubutu
Banda magana, rubutu shi ne akasari jama’a ke amfani da shi wajen sanar da juna abubuwan da suke yi musamman a ɓangaren kasuwanci da kuma yin yarjejeniya tsakanin ƙasashe. Saboda haka, rubutu kan bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, ya kuma haɗa kan ƙasashe daban-daban idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.
Hanya ce ta ilimantar da jama’a.
A ɓangaren watsa labarai ko na gidajen rediyo ko kuma na jaridu, rubutu shi ne tushensu.
Rubutu na iya kawo gaba tsakanin mutane har da ƙasashe in ba a yin amfani da shi yadda ya kamata ba. Yakan ɓunkasa zaman lumana.
Kome a rubuce kan ɗauki tsawon lokaci kafin ya ɓace. Da wuya a ne musunta shi.
Ta hanyar rubutu muke sanin abin da ya faru a baya da kuma samun ilimin da muke amfani da shi a yau, shi kuma muke amfani da shi wajen shirya na gobe.
Tambayoyi
Me ake nufi da kalmar rubutu?
Lissafa kashe-kashen rubutu da muke da su.
Yi bayani mai gamsarwa a kan rubutun insha’i da rubutun wasiƙa.
Kawo Muhimmancin rubutu guda biyar?
Share with your friends: |