Kashe-Kashen Rubutu
Abubuwan da ake amfani da fasahar rubutu wajen gudanar da su, Sun haɗa da: Shifta da rubutun rahoto da rubutun insha’i da rubutun labari. Ga bayani a kan su, ɗaya bayan ɗaya.
Ana yin sa ne don a ceci lokaci, watau a maimakon malami ya yi rubutun a kan allo don yara su juya a takardunsu sai ya riƙa karanta musu, su ma suna rubutawa a takardunsu. Duk abin da kowanne ɗalibi ya rubuta nasa ne, saboda haka, wajibi ne:
ya saurari malamin da kyau kada ya rubuta shirme.
ya riƙe muhimman abubuwan da laccar ta ƙunsa.
Ya koyi yadda ake taƙaita kalmomi watau (abbreviation).
Ya lura da bayala (margin)
A ƙarshen darasin, yana da kyau ya samu lokaci ya gyara kura-kuren da ke cikin rubutun.
Kamar yadda sunan ya nuna, wannan kashin rubutu ne inda ake ba da muhimman labarin abin da ya faru musamman a taro. A rubutun rahoto, babu maganar ƙarin gishiri.
Jawabi shi ne rubutun da aka rubuta a kan wani batu na musamman da niyyar karantawa a taron jama’a. Saboda haka, yana da kyau marubuci ya kula da irin matsayin mutanen da za su saurare shi ko karanta jawabinsa. Da dalilan rubuta jawabin.
Insha’i labari ne da aka ƙirƙiro a kan wani batu na musamman wanda aka rubuta shi cikin natsuwa ta hanyar kula da ƙaidojin rubutu da kuma yin amfani da salon sarrafa harshe da salon rubutu mai armashi. Irin wannan labari na iya kasancewa a kan addini ko siyasa ko tattalin arziki ko sana’a ko biki ko ilimi ko yaƙi ko gaba da makamatansu. Akan rubuta insha’i don a ga ƙwarewar marubuci wajen amfani da harshe.
Insha’i ya kasu kashi uku kamar haka:
Insha’i na labari
Insha’i na bayani
Insha’i na Muhawara.
Rubutu ne da ake yi don sanar da wani halin da ake ciki. Yana iya kasancewa tsakanin babba da na ƙasa da shi ko kuma tsakanin abokai ko kuma abokin ciniki. Sau da yawa, akan rubuta wasiƙa ne don neman taimako.
Share with your friends: |