Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa



Download 0.59 Mb.
Page9/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
Alamomin rubutu

Alamomin rubutu su ne ayoyin da ake amfani da su a cikin kowane irin rubutu don rubutun ya samu karɓuwa ga makaranta. Rashin yin amfani da su yadda ya kamata kan iya kawo ruɗani da rashin gane manufar magana, ko jimla sosai. Don haka, wajibi ne a kawo su tare da misalai.



Kashe-kashen Alamomin rubutu:

Alamomin rubutu sun haɗa da, alamar tsayawa da alamar waƙafi da alamar waƙafi mai ruwa biyu da alamar baka biyu da alamar tambaya da alamar motsin rai da karan-ɗori da alamar zacen wani.



  • Alamar Tsayawa (.) Akan yi amfani da aya ne, idan an kammala rubuta wani matsayin, ko ƙarshe na tunani. Misali: Audu yana zaune a Ikko.

  • Alamar Waƙafi (,) Akan yi amfani da wakafi ne don mai karatu ya tsaya ɗan kaɗan, ya ja numfashi. Misali Ko an kashe biri, ya riga ya yi ɓarna.

  • Alamar waƙafi mai ruwa biyu (;) Akan yi amfani da wannan waƙafi don a raba waɗansu ɓangarori na jimla mai tsawo; waɗanda waƙafi ba zai iya raba su sosai ba. Misali, Yara kan so, su yi wasa da tsalle-tsalle; manya kuwa kan so su zauna abinsu a ƙofar gida.

  • Alamar baka biyu (()) Akan yi amfani da baka guda biyu ne, domin a tsame, ko keɓe wata kalma, ko magana, wacce tsame ta, ko cire ta, ba zai lalata ma’anar jimla ba. Irin kalmar ko harafi da akan tsame takan ƙara wa jimla kyau ko armashi. Misali; Mutumin nan (mai ‘yan uku-uku a fuskarsa) bai sake komowa ba tun ranar nan. Suna (Bala da Babiya) cikin ɗaki.

  • Alamar tambaya (?) Ita wannan akan yi amfani da ita ne, don neman bayani ko labari. Misali; Yaushe ka dawo? Ko ka je Makaranta jiya?

  • Alamar motsin rai (!)Akan yi amfani da ayar motsin rai a ƙarshen jimla ko kalma don a ƙarfafa magana ko don a nuna tausayi ko ƙiyayya ko soyayya ko tsoro ko firgita ko farin ciki da sauransu. Misali; Wayyo Allahna! Ya Lalace! Kaico! Kash!

  • Alamar karan-ɗori (-) akan yi amfani da shi ne wajen haɗa kalmomi guda biyu ko fiye da haka domin su ba da ma’ana guda daya. Misali; Yau-da-gobe sai Allah. Na hange shi yana tafiya da sauri-sauri.

  • Alamar zacen wani (“ )Akan sa ta ne a jikin kalmar mutum ta farko daga hagu wato an buɗe maganar da ya yi da bakinsa ke nan ba da bakin wani ba. Haka kuma akan yi amfani da ita wajen rufe maganar wani. Misali; Dawaki ya ce da maigoro, “Zan tafi Akure gobe in Allah ya so”.


Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page