Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa


{a’idojin Haɗa Kalma Ko Rabawa



Download 0.59 Mb.
Page10/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
{a’idojin Haɗa Kalma Ko Rabawa

A ƙarƙashin wannan kashi za mu ga bayani a kan abin da ake nufi da haɗa kalma da raba kalma, sai kuma ƙa’idoji na raba kalma da na haɗawa.



Haɗa Kalma

Ibrahim (2001) ya bayyana cewa idan aka haɗa kalmomi biyu ko fiye da haka, aka mai da su abu ɗaya ma’anarsu za ta canza, domin yin haka zai canza lafazin kalmar, har ma jan baki da ke cikin kalmomi zai canza.

Saboda haka dole ne kalmomin da suke a haɗe a bar su yadda suke don samun daidaito ga ma’ana da lafazi, waɗanda suke a rabe kuma a bar su a hakan.

Raba Kalma

Kamar yadda bayani ya zo a karatu da rubutu a Harshen Hausa, raba aiki na ɗaya daga cikin ayyukan da suka wajaba a kan kowanne mai rubutu. Aiki ne na ciccire sheɗara a mai da haruffan da ke cikinta ƙungiya-ƙungiya. Daga ƙungiyoyi, waɗansu za su kasance kalmomi ne, waɗansu kuwa haruffa. Duk da haka, aikin sunansa raba kalma ba raba harruffa ba.




Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page