Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa


(e). Kalmomi Masu Yi Wa Mutum Gizo



Download 0.59 Mb.
Page12/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
(e). Kalmomi Masu Yi Wa Mutum Gizo

Yana da kyau mai rubutu ya kula da kalmomin nan masu gizo domin yawanci sukan rikitar da mai karatu. Ga su nan a ƙasa:



  1. Ba’a Da Ba a

Misalan ba’a;

  • Suna ta ba’a ana dariya.

  • Yaro ya iya ba’a.

Misalan ba a:

  • Ba a fafe gora ranar tafiya.

  • Ba a fitsari a nan.

  • Ba a zama a nan.

  • Jeka ba a tsaya a nan.

(ii) Akan Da A Kan

Misali:


  • Sai an ciza akan busa.

  • A nan akan tashi

  • Akan biya shi kuɗinsa.

Wajen amfani da a kan kuwa ta bambanta.

Misali:


  • aza abincinsa a kan tebur.

  • Suna zaune a kan gado

  • Ya kwanta a kan darduma.

(iii) DAKA DA DA KA

Misalan daka:



  • Tana daka da waƙa.

  • Mai laifi za a daka.

  • Ya daka a guje.

Misalan da ka:

  • Ba mu aiki da ka.

  • Ya yi karatu da ka

  • Ya faɗo da ka.

(iv). SA’A DA SA A

Misalan Sa’a:



  • Ya samu sa’a

  • Sa’a ce

  • Sa’arta ta fi ta tsawo.

  • Ya gama a sa,a ɗaya.

Misalan Sa a:

  • Ya sa a kama shi.

  • Ban sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.

  • Za mu sa a biya.

(v). DAWA DA DA WA

Misalan Dawa



  • Ya yi nomar dawa.

  • Ya tafi dawa.

  • Dawa

Misalan Da Wa

  • Da wa suka zo.

  • Da wa aka haɗa shi.

  • Ko ka san da wa suka iso?

(vi). Gashi Da Ga Shi

Misalan Gashi:



  • Gashi

  • Gashi ya ƙone

  • Gashin ya yi yawa.

Misalan Ga shi:

  • Ga shi.

  • Ga shi can a zaune.

  • Ga shi a ba shi.

(vii). Gata Da Ga ta

Misalan gata:



  • Gata

  • Gata za su zo

  • Musa ɗan gata ne.

Misalan ga ta:

  • Ga ta

  • Ga ta nan zuwa

(f). Jakada ‘wa’ da dafa-keya ‘wa’.

  1. Jakada ‘wa’ yana biyo bayan aikatau ne.

Misali:

  • Sun cinye wa Ladi tuwo

  • Ta kama wa sani Akuya.

Idan muka lura da kyau za mu ga ba a liƙa ‘wa’ da kalmomin aikatau da suke gabace su ba. Yin haka kuskure ne.

  1. Dafa-keya ‘wa’

Wannan ‘wa’ ɗin liƙa wa aikatau ake yi don a samar da suna. Misali:

Cinyewa suka yi

Jefawa suka yi d.d.s

(g). Kada A Haɗa Kalmar Suna Da Ganga-Dogarau

Ba a haɗa kalmar suna da ganga-dogarau ko da akwai haraffin madanganci a bayan kalmar sunan da kalmar ganga-dogarau ɗin ke bi. Misali:



  • Maganar da ba maganarda ba.

  • Rigar da ba rigarda ba.

  • Yarinyar da ba yarinyarda ba.

(h).Kalmomin Karan-Ɗori

Karan-ɗori (-) wata alama ce da ake sakawa tsakanin kalmomi biyu ko fiye domin su ba da ma’ana ɗaya. Rashin amfani da karan-ɗori tsakanin kalmomi kan sa su tashi a matsayin jimla.

Misali:

- Tuma – ƙasa

- Faɗi – ka – mutu

- Gaya-wa-jini-na-wuce.



(i). Nanata Baƙaƙe Masu Goyo

Wajen rubuta su dole ne a nanata haraffin farko na baƙaƙe masu goyo ga wasu baƙaƙe.

Misali:

Kyakkyawa ba kyakykyawa ba

Fyaffyace ba fyafyfyace ba

Shasshere ba shashshere ba.



Tambayoyi

  1. Me aka nufi da ƙa’idojin rubutu?

  2. Lissafa alamomin rubutu da muke da su. Sannan, yin cikakken bayani a kan uku daga cikin su.

  3. Yi bayani mai gamsarwa a kan rubutun insha’i da rubutun wasiƙa.

  4. Ku sake rubuta wannan shafi yadda ya kamata a karɓaɓɓiyar Hausa:

Wa san kwai kwayo wasane da ake gina shikan kwaikwayon wani labari, ko wata matsala tarayuwa da ake son nusar wa ga jama’a. Rabe-Raben wasan kwaikwayo sun haɗa da, rubutaccen wasan kwai kwayo da rubutattun Waƙoƙi da rubutu n zube.

Fasali Na Biyar

Karatu a aikace:

Gabatarwa

An karkasa wannan fasali zuwa kashi biyu, a kashi na ɗaya akwai misalin hira watau tattaunawa, a kashi na biyu, akwai wani labari mai gutsuren shafi.



Manufa:

Manufar wannan fasali ita ce, ana so a gane ƙwarewar ɗalibai wajen karatu da kuma fahimci abin da suka karanta.



Kashi Na Ɗaya - Karanta hira ko tattaunawa mai ɗan tsauri

Hira zance ne tsakanin mutane, yana iya kasancewa tsakanin babba da na ƙasa da shi ko kuma tsakanin abokai. A nan ƙasa za a kawo misalin hira ne tsakanin abokai wanda ɗalibai za su karanta ƙarƙashin jogorancin malami wanda zai riƙa gyara musu kura-kuren da za su iya yi.



Hira Tsakanin Mai Saye (Ademokoya) Da Mai Sayarwa (Ige)

Yanzu muna kasuwar Oja-Oba a garin Ikere –Ekiti inda malam Ademokoya ke sayen doya. Ga Ige, yana tsaye a gaban Ademokoya, yana son ya sayi doya a wajen sa. To! Bari mu yi kusa da su mu ji yadda hira za ta kasance.

Ige: Malam, barka kadai.

Ademokoya: Yawwa, barka da zuwa.

Ige: Yaya kasuwa?

Ademokoya: Alhamdu lillahi.

Ige: Kana da doya?

Ademokoya: Eh! Da yawa ma.

Ige: Yawwa, nawa ne kashi ɗaya?

Ademokoya: Naira dubu biyu da ɗari biyar.

Ige: Haba malam! Doyarka na da tsada.

Ademokoya: Bai tsada ba, abin ya kasance haka saboda rashin man fetur.

Ige: To! Zan biya dubu ɗaya da ɗari bakwai.

Ademokoya: Albarka.

Ige: Nawa za ka rage mani?

Ademokoya: Zan rage ma ka ɗari biyar.

Ige: To? Idan haka ne, za ka ba ni manya- manya ko?

Ademokoya: Babu laifi.

Ige: Ka kawo su in gani.

Ademokoya: Ga su nan

Ige: Kai! Sun yi mani kaɗan, bana saya sai ka yi mani kyautar doya guda tun da yake ni abokin kasuwa ne a gare ka.

Ademokoya: Zan ƙara ma ka.

Ige: Ga kuɗi.

Ademokoya: Saura naira ɗari.

Ige: Ba zan ƙara komai ba.

Ademokoya: Shi kenan

Ige: Allah ya amfani.

Ademokoya: Amin, je ka ɗauke su.

Ige: Na gode, sai gobe.

Ademokoya: Yawwa, sai mun sake haɗuwa.



Kashi na biyu - karatun gutsuren shafi.

A wannan kashi, malami zai riƙa kiran yara ɗaya bayan ɗaya su karanta labarin da ke ƙasa kuma ya gyara musu kura-kuren da suka yi. Sannan su amsa tambayoyin da ke biye

LABARIN ‘YAN KURCIYA MARAS HANKALI

Waɗansu ‘yan kurciya guda biyu suka zaɓi wuri, za yi sheƙa. Sai wata ta zo ta ce, “Ku tashi! Gidana ne”. Suka ce, “Ba za mu tashi ba, domin mu riga ki zuwa.” Ta ce, “Yaya kuka riga ni? Ai ku yara ne, bara da bara wancan duk nan na yi sheƙata.”

Sai suka kama faɗa, har da fige-figen gashi. Ba su sani ba, ashe Kyanwa tana maƙe tana kallonsu. Da ta ga hankalinsu ya rabu da su, sai ta yi ɓut ta danne su duka uku, ta cinye. Ba wanda ya sami gidan.

TAMBAYOYI



  1. ‘Yan kurciya guda nawa ne?

  2. Me suka ce ma kurciya ta uku?

  3. Me ta gaya musu?

  4. Wa ke maƙe tana kallonsu?

  5. Me ya faru tsakaninsu?


Fasali Na Shida

Rubutu A Aikace

Gabatarwa

An karkasa wannan fasali zuwa kashi uku, kowanne kashi na da hotunan da malami da yara za su yi aiki a kan su.



Manufa:

Manufar wannan fasali ita ce, ana so a gane ƙwarewar ɗalibai wajen rubuta ra’ayinsu da Hausa, musamman yin amfani da ƙaidojin rubutun Hausa inda suka kamata.



Kashi Na Ɗaya - Shifta

A wannan kashi, malami zai riƙa furta sunayen abubuwan da ke cikin hotunan da ke ƙasa a yayin da yara za su riƙa rubuta su a takardunsu.shi malami, zai riƙa gyara masu kura- kuren da suka yi.

H

oto na ɗaya





Hoto na biyu

Hoto na uku





Kashi na Biyu: Rubutun saukakan jimloli.

A wannan bangare, yara za su duba hotunan nan da ke sama bi da bi a hankali, sannan za su rika gina saukakkun jimloli a kan kowannensu bisa umurnin da malami ya ba su.



Kashi na Uku: Rubutun guntsuren labari.

  1. Dubi wannan hoto a hankali, sannan ka rubuta labari da ba zai gaza kalmomi ɗari ɗaya da hamsin ba.

Hoto na huɗu



B (i) To! nan ina ne kuma me ake yi?

Hoto na biyar



B (ii) Rubuta labari wanda ba zai gaza kalmomi ɗari biyu da hamsin a kan makarantarmu.

(c). Rubuta labari da bai gaza shafi ɗaya ba a kan wannan hoto.

Hoto na shida





MANAZARTA

Bargery, G.B (1993). A Hausa - English Dictionary and English - Hausa Vocabulary.

Zaria. ABU, Press.

Calvin Y.G (1984) Nazarin Hausa: A {ananan Makarantun Sakandare littafi Na Farko.

Ikeja, Lagos. Nelson Pitman Limited.

Charles Scribner Jr. (1991). In the Company of writers: A life In publishing. New York City. Charles Scribner’s Sons.

Ibrahim I.Y Da Abdulƙadir, D (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria. Gaskiya Corporation

Limited.


Ibrahim I.Y (1988). Hausa A Rubuce. Zaria. Northern Nigerian Publishing Company.

Ibrahim M. (2001) {a’idojin Rubutun Hausa Don Ɗalibai, Marubuta da Masu Nazari.



Ahamadu Publishing Network

Ibrahim, Y.K and Ige, O.D. (2006):”Auna Fahinita a Sauƙaƙe” in Y. A. Babatunde (ed)

integrated language and literary studies ii. Al-bas international publisher Lagos

Ige, O.D, (2010): “Rubutun Insha’i” in Y. A. Babatunde (ed) Readings in Language and Literature. AL-bas international Publisher.

Ilesanmi Press (Nig.) Limited (1976) Mu Koyi Ilmin Halitta Da Kiwon Lafiya Da Kimiyya Littafi Na Biyu. Ilesa.

Mortimer J.A and Charles V. D (1940). How to Read a Book: How to Read a Book: The classic Guide to Intelligent Reading. New York City. Touchstone.

Neil Skinner (1965). {amus na Turanci Da Hausa. Zaria. Northern Nigerian Publishing

Company.


Seweje, E.O (2005). A Comprehensive Approach to communication in English Language. Ikeja, Lagos. Atlantic Associated Publishers.

Usman, A.Z (2011). Matsalolin Rubutu Da Harshen Hausa: Tsokaci A kan {a’idojin.



Raba Kalma da Haɗawa. Being a paper presented at 3-day National Workshop 3rd -5th May, 2011 on Writing in Nigerian Languages at institute of Nigerian Languages, University of Nigeria. Aba Campus.

www.slidesshare.net/orlantho/types-of-reading Retrieved on 05/07/2013.

www.merriam-webster.com/.. /writing



www.slidesshare.net/orlantho/types-of-reading Retrieved on 19/07/2013.

www.merriam-webster.com/../writing Retrieved 09/08/2013.

Wikipedia (2013). http://www.en.wikipedia.org/../Reading_(process). Retrieved on

09/08/2013.

Yusufu Yunusu (1987). Rubutun Wasiƙa A Dunƙule. Zaria

Northern Nigerian Publishing Company.



Zarruk, R.M (1980). Lafazin Hausa A Taƙaice. ABU, Zaria. Institute of Education



Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page