Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa


{a’idojin Raba Kalma Da Na Hadawa



Download 0.59 Mb.
Page11/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
{a’idojin Raba Kalma Da Na Hadawa

Wajibi ne ga mai rubutu ya kula da ƙa’idojin raba kalmomi da na haɗawa. Yin haka zai taimake shi wajen yin rubutu mai ma’ana kuma wanda zai samu karɓuwa ga makaranta. To! Yanzu bar mu fara yin bayani a kan ƙa’idojin bi da bi:

(a). Kalmomin Mallaka:

Wannan iri biyu ne, akwai gajerar Mallaka da doguwar Mallaka. Kuma mallaka ta shafi abu biyu, wato mai Mallaka da abin da aka Mallaka.

Gajerar Mallaka a koyaushe tana liƙe ne da sunan mai Mallaka. ( -nka, -nki, -nku, -rka -rki -rku d.s). Ga misali:

Littafinka

Wadonka

Tulunki


Takardarka

Rigarka d.d.s

Ita doguwar Mallaka ba a liƙa su da wata kalma. Ga yadda ake rubuta su ( nawa, naka/ki, nasa, nata, namu, naku, nasu, tawa, taka/ki, tasa, tata, tamu, taku da tasu)

Littafi nawa

Gida naka/ki

Takalma naku

Riga tawa

Akuya taka

Mota taku

Abinci namu d.d.s

(b). Rubuta Lokutan Hausa, wannan guda takwas ne.

Idan an zo rubuta lokutan Hausa, dole ne a haɗa wakilin sunansu da lokacinsu sai dai a wuri biyu kawai, wato wurin lokaci mai zuwa, inda lamirin lokaci kan gabaci lamirin suna, saboda haka, dole ne a raba su, sai kuma wurin sigar makasudi ko kuma togaciya inda lamirin suna kawai ake samu babu lamirin lokaci



  • Lokaci mai Zuwa.

Wannan aji ne ake raba lamirin lokaci daga lamirin sunan idan aka zo rubutu na yau da kullum, kuskure ne a haɗa su.

Misali


Za na (zan)

Za ka


Za ki

Za ya (zai)

Za ta

Za mu


Za ku

Za su


  • Sigar Makasudi ko Togaciya.

Wannan ajin bai da lamirin lokaci, saboda haka, lamirin suna kadai ake rubutawa.

Misali:


Na o

Ka o

Ki o

Ya o

Ta o

Mu o

Ku o

Su o

Misalansu a jimla:

Na karanta

Ka karanta

Ki karanta

Ya karanta

Ta karanta

Mu karanta

Ku karanta

Su karanta

(c). KALMOMI MASU GAƁA ƊAI-ƊAI

Kalmomi masu gaɓa ɗai-ɗai, ana rubuta su a ɗai-ɗai ɗinsu ne a jimla. Haɗe su na ɓata rubutu kamar su: su, ne, ta, shi, kai ke, zo, ci, bi d.d.s

Ya ce zai je can yau.

Da can ya san ta.

An ta da shi.

(d). Raba Kalmar Wakilin Suna Da Ta Suna Daga Kalmar Dirka

Wajibi ne a raba wakilin suna da ta suna daga kalmar dirka idan suka fito jere a cikin jimla. A kullum kalmar dirka a rabe ake rubuta ta ba a haɗe ta da wata kalma a rubutu.

Misali; Shi ne ya zo ba shine ya zo ba

Audu ne ba Audune ba

Taka ce ba takace ba

Wasu ne ba wasune ba

Yaro kenan ba yarokenan ba d.d.s


Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page