Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa



Download 0.59 Mb.
Page4/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
Fasali Na Uku

Rubutu Da Kashe - Kashensa

Gabatarwa

Rubutu wani hanyar sadarwa ne wanda Bil Adama yake amfani da shi wajen bayyana ra’ayinsa game da wani batu wanda yana iya kasancewa ya watsar da addini ko labari ko ilimi da makamatansu ga abokan zamansa ko kuma alumma baki daya. Saboda haka, yin rubutu na bukatar marubuci da ya kasance wanda ya nazarci harshen da zai rika amfani da shi ciki da waje musamman nahawunsa, kaidojin rubutunsa da kuma yadda ake sarrafa shi. Banda haka, dole ne ya yi rubutun cikin natsuwa da kuma kwanciyar hankali ta yadda duk wanda ya karanta rubutunsa zai gane shi ba tare da shan gumi ba.



Manufa

A karshen wannan fasali ana sa rai dalibai za su iya:



  1. Bayyana kalmar rubutu.

  2. Faɗi kashe-kashen karatu.

  3. Yi taƙaitaccen bayani a kan kowanne kashi.

  4. Bayyana muhimmancin rubutu.

Ma’anar Rubutu

Rubutu wata sababben hanya ce inda ake yin amfani da sanannun alamomi wajen isar da saƙo ba tare da yin magana ko kuma yin amfani da sassan jiki ba. Rubutu na iya kasancewa a kan takarda ko katako ko dutse.

Harkar rubutu abu ne wanda yake bukaci marubuci ya kasance mai yin bincike da zurfin tunani a kan abin da ya bincika da kuma yin amfani da kalmomi inda suka dace, su kuma fito da ma’ana.

A taƙaice, rubutu abu ne da ke bukatar marubuci ya tsara tunaninsa dalla-dalla kuma ya yi amfani da salon rubutu mai armashi waɗanda za su sa makaranci ya ji daɗin karantawa da kuma gane abubuwan da ke cikin littafinsa ba tare da ɓata lokaci ba.




Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page