Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa



Download 0.59 Mb.
Page3/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
Fasali Na Biyu

Nau’o’in Karatu

Gabatarwa

Kamar yadda muka gani a fasali na ɗaya, karatu yana da matukar muhimmanci ga kowanne Bil Adama wanda yake son ci gaba musamman wajen bunƙasa iliminsa, saboda haka yana da kyau mun yi bayani a kan nau’o’in karatu. Wannan zai taimaka wa makaranci wajen gane duk abin karantawa da ya sa a gaba cikin sauƙi.



Manufa:

A ƙarshen wannan fasali ana son ɗalibi ya iya bayanna nau’o’in karatu da kuma gane yadda zai yi amfani da su a yayin karatu.



Nau’o’in Karatu

Masanan harshe sun karkasa karatu zuwa kashi biyu bisa dalilin yin karatu da kuma yadda ake yin karatun.

Broughton d.s.s (1978) da Oyinloye (1996) Sun karkasa karatu zuwa gida biyu kamar haka:


  1. Karatu cikin Natsuwa (Intensive Reading).

Wannan nau’in karatu ne inda makaranci ke karanta littafi/labari cikin natsuwa domin ya fahimce shi ciki da waje. Sau da yawa ya yiwu ana bukaci makaranci ne ya fitar da muhimman saƙo ko kuma jigo. Irin wannan nau’in karatu ne aka fi yin amfani da shi wajen nazarin auna fahimta.

  1. Karatu na sama-sama (Extensive Reading watau).

Wannan nau’in karatu ne inda makaranci ke karanta labari sama-sama kuma cikin sauri da niyyar samun taƙaitaccen bayani a kan abin da labarin yake magana a kai. Yana yi ne don nishaɗi ko kuma don ya ƙaru. Mutane sun fi yin amfani da wannan nau’in karatu a wuraren sayar da jaridu.

Waɗannan nau’o’i na karatu su ne akasarin masana suka fi magana a kai. Amma banda su akwai wasu, irin su:

Karatu cikin gaggawa (fast reading) :

Shi ne inda makaranci ke karanta labari da sauri cikin rashin natsuwa, yana yi ne kawai ba da niyyar ya fahimci labarin ciki da waje ba.

Sai karatu na kalma a matsayin kalma (word for word): Kamar yadda sunan ya nuna nau’in karatu ne inda makaranci ke ɓata lokaci don yakan dubi kalma sau biyu ko fiye da haka kafin ya gane nufin marubuci, wani lokaci ya sake karanta jimlar da ya riga ya wuce, wannan kan faru ne a sakamakon rashin kwanciyar hankali da kuma rashin sha’awa ga abin da yake karantawa.

Tambayoyi


  1. A naka fahimta, me ake nufi da nau’o’in karatu? Ya kasu kashi nawa?

  2. Kawo nau’o’in karatu da muke da su.

  3. Bayyana aƙalla biyu daga cikin nau’o’in karatu.

  4. A ra’ayinka wane nau’i ne kake ganin zai fi kyau ga dalibin da yake shirin rubuta jarrabawa?



Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page