Fasali na Ɗaya Ma’anar Karatu da dalilan Yin Karatu. Gabatarwa



Download 0.59 Mb.
Page1/12
Date20.10.2021
Size0.59 Mb.
#57501
  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION
HAU 212 COLLEGE SERIES CORRECTED VERSION

Fasali na Ɗaya

Ma’anar Karatu DA Dalilan Yin Karatu.

Gabatarwa

Karatu wani muhimman ɓangare ne na neman ilimi, saboda haka, yin karatu yakan zurfafa tunanin mai yi domin zai fahimci abin da marubuta ko mawallafa suka rubuta.wannan fasali na ƙunshe ne da bayanai a kan karatu da dalilan yin karatu:



Manufa

A }arshen wannan fasali ana sa rai ]alibai za su iya bayyana kalmar karatu da lissafa dalilan yin karatu aƙalla guda uku da kuma yin cikakken bayani a kan biyu daga cikin dalilan da suka rubuta.



Ma’anar Karatu.

Masanan harshe sun yi ƙoƙari wajen bayyana kalmar karatu ta hanyar da ake aiwatar da shi kamar haka:

Karatu hanya ce da makaranci ke bi domin ya gane tunanin marubuci ko mawallafi wanda ya rubuta a kan takarda ta hanyar amfani da sanannun alamomi.

Charles (1991) ya ce karatu hanya ce ta yin tunani tare da marubuci a kan abin da ke zuciyarsa. Yakan faɗaɗa tunanin makaranci wajen gane saƙon da marubuci yake so ya isar ga jama’a.

Mortimer da Charles (1940), a littafinsu mai take ‘How to Read a Book: The classic Guide to Intelligent Reading’ sun bayyana cewa karatu hanya ce inda makaranci ba ya dogara a kan komai fiye da sannanun alamomi da ke cikin abin da yake karantawa ta hanyar amfani da basirarsa wajen gane abin da rubutun ke magana a kai.

Banda waɗannan ana iya cewa karatu sabon hanyar sadarwa ce inda ba lalle ne marubuta da makaranta su ga juna ƙiri-ƙiri kafin su isar da saƙo ta musamman dangane da abin da ya faru ba. Sau da yawa karatu yakan bukaci makaranci ya yi amfani da tunaninsa wajen gane abin da ya karanta.

A ra’ayina, karatu shi ne duba abin da aka rubuta ko a kan takarda ko allo ko katako ko kuma dutse da niyyar fahimtar abin da rubutun ke magana a kai ta hanyar amfani da basirarsa.


Download 0.59 Mb.

Share with your friends:
  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12




The database is protected by copyright ©ininet.org 2024
send message

    Main page